Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyar PDP Ta Kalubalanci Kashe Dala Biliyan Daya Kan Aikin Gada A Jihar Katsina


Gwamna Aminu Bello Masari (Facebook/Bello Masari)
Gwamna Aminu Bello Masari (Facebook/Bello Masari)

Batun ciyo bashin kimanin naira biliyan guda da gwamnatin jihar Katsina tayi wadda take gudanar da aikin gina gadojin sama dana kasa a birni da kewayen Katsina na ci gaba da fuskantar caccaka daga ‘yan hamayya.

Hakan na zuwa ne adai-dai lokacin da tsohon sakataren gwamnatin jihar Dr Mustafa Inuwa ke korafin mayar dashi sanaiyar ware a harkokin Jam’iyyar APC mai mulkin jihar tun bayan daya sha kaye a zaben fidda gwani na gwamnatin jihar.

Ga alama dai har yanzu zaben fidda gwani na dan takarar gwamnan Katsina a Jam’iyyar APC ya bar baya da kura, domin kuwa wasu daga cikin wadanda suka sha kaye a zaben ne ke ci gaba da korafin mayar dasu saniyar ware, tun bayan kammala zaben.

Dr Mustafa Inuwa, tsohon sakataren gwamnatin jihar ta Katsina kuma shugaban farko na jam’iyyar ta APC a jihar na cikin jerin ‘yan takarar kimanin 8 da suka nemi jam’iyyar ta basu tikitin takarar gwamnan jihar a zaben badi, amma basu sami nasarasaba. Yace basu yi zaton cewa, za ayi wani al’amari da zai kawo nakasu a tafiyar su ba, amma sai aka wayi gari ana tafarkin mayar dasu saniyar ware tare da magoya bayan su, domin kuwa tun baya zaben tuntuba ma ya gagara, baya ga kora da hali da ake yiwa magoya bayan su.

Wannan ta sanya masu kula da lamura ke cewa, akwai babban kalubale a gaban APC ta Katsina amma mataimakin shugaban Jam’iyyar a jihar Alhaji Bala Abu Musawa na cewa, tun bayan kammala zaben fitar da gwani a Jam’iyyar ta APC inda aka zabi dan takaar gwamna, hankula sun koma ne kan harkoki da tsare tsaren zaben dan takarar shugaban kasa a can Abuja, kana daga bisani aka tafi aikin hajji da kuma bubukuwan sallah. Sai dai bayan haka an kira taruka da ‘yan takara karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari kuma an yi kalaman na ban hakuri ga wadanda ba su sami nasara ba, kuma an amince za’a tafi tare domin cin nasara.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da 'ya'yan jam’iyyar PDP a jihar ta Katsina ke kushe bashin da gwamnatin jihar ta ciwo na kimanin naira miliyan dubu 8 da ake aiwatar da ayyukan gina kadoji guda uku a birnin Katsina.

Hon Zahradeen Babba-Mazoji wani jigo a Jam’iyyar PDP a jihar Katsina, yace yayin da gwamnati ta ciwo bashi domin gina Gadoji, ‘yan fashin daji ne ke jerin gwano da Babura suna kai farmaki kauyuka da Garuruwa na sassan jihar Katsina, a don haka kamata yayi gwamnatin Katsina ta ciyo bashi domin samar da kayayyakin aiki ga jami’an tsaro da zasu murkushe ayyukan ‘yan ta’adda, maimakon gina gada.

Duk kokarin da Muryar Amurka ta yi na jin ta bakin Kwamishinan ayyuka na jihar dangane da wannan batu na aikin gadojoji ya cimma tura.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG