WASHINGTON, DC —
Shugaban jam'iyyar APC na kasa Chief Bisi Akande ya ce muddin 'yan Najeriya suka cigaba da bautawa kudi da abun duniya babu yadda kasar zata cigaba.
Chief Bisi Akande ya ce a gaskiya idan ya duba baya sai ya ji ransa ya baci domin Najeriyar da ta fi ta yau. Idan aka dubi fannonin rayuwa daban daban na wancan lokacin Najeriya ta wuce yadda take yau. Daga shekaru 25 ne abubuwa suka fara lalacewa lokacin da kudi ya fara zama Allah da 'yan kasar ke bautawa.
Kan tabarbarewar kasar ya ce kada a dorawa su 'yan siyasa laifi. A dorawa sojoji da suka yiwa mulkin kasar katsalandan. Sojoji ne suka kawowa kasar matsala domin su ba'a horas da su yadda ake mulki ba. Abun da aka koya masu shi ne kare martabar kasa. Kuma duk abun da ba'a koyawa mutum ba da zara ka shigeshi kana iya yin kuskure.
Dangane da cewa idan sojoji suka hambare gwamnati nuna anfani da 'yan siyasa wurin yin mulkin kasar domin haka suna da laifi. Chief Bisi Akande ya ce baya tunanin 'yan siyasa nada laifi domin idan da basu yiwa mulkin kasar katsalandan ba to sai a ce duk abun da ya faru laifin 'yan siyasa ne. Kuma kada a manta siyasa abu ce dake da nasaba da ra'ayoyin al'umma daban daban kuma haka tsarin Najeriya yake. Ya ce lokacin da suka fara mulki a matsayin 'yan siyasa suna koyo ne. Basu kware ba. Abun da mutum yake koyo domin ya yi kuskure bai kamata a ga laifinsa ba nan take. Ya ce suna cikin koyon ne kwaram sai sojoji suka yi juyin mulki. Domin haka 'yan Najeriya su ga laifin sojoji da suka yi katsalandan kan abun da ba nasu ba kuma ba'a horas da su ba a kai.
Yanzu shekarau 48 da aka yi juyin mulkin farko amma kasar bata kai inda ya kamata ta kai ba. Amma duk da abubuwan nan a akwai haske domin idan lokacinmu bamu ga cigaban da yakamata a samu ba na baya masu tasowa rayuwarsu ta sha ban ban da namu. Ba kamar namu rayuwar ba da muka yi cikin duhu da kauyanci, zuri'ar yau suna ganin abubuwan dake faruwa a wasu kasashe ta duniyar gizo da sauran hanyoyin sadarwa. Yanzu da wuya a yi masu rufa rufa. Kansu ya waye dominabubuwan da suke gani kuma suke karantawa.
Ga shawara ga 'yan Najeriya. Su jingina baiwa kudi fifiko. Su nemi martaba da kima. Abun da kudi zasu saya suke da mahimmanci. Kada su yadda kudi ya zame abun bautansu domin mu 'yan kasar mun koma kudi muke bauta wa. Idan baka dasu ka zama banza dalili ke nan kowa na rububin ya tarasu.
Ga cikakken rahoto.