Barrow dai ya komagida ne daga kasar Senegal inda ya zauna tun bayan da rikicin siyasa ya barke a kasarsa, saboda shugaban kasar Jammeh wanda ya dade yana mulkin kasar, yaki saukabayan da yasha kaye a zaben watan Disambar bara.
Jirgin da Shugaba Barrow ya shigo zuwa kasar tasa, sojojin Senegal dana Najeriya ke gadin sa, jim kadan da saukar sababban birnin kasar wato Babjul, inda daruruwan ‘yan kasar ne suka yi masa lale marhabin.
Wani dan jarida da ya gane wa idanun sa isowar shugaba Barrow, yace tun kafin isowar sa ne ‘yan kasar suka yi cincirindo kan hanyar zuwa filin jirgin saman kasar suna ta raye-raye da wake wake.
Mai Magana da yawun hadakar jamiyyun da Barrow yayi takara karkashinsu yace ko baya ga wannan tarbon akwai wani na musammam da aka shirya.
An dai rantsad da Barrow ne a matsayin sabon shugaban kasar a ofishin jakadancin Gambia dake kasar Senegal a cikin makon da ya gabata.
Yanzu haka dai sojojin kasahen kungiyar ECOWAS zasu ci gaba da kasancewa kasar ta Gambia har na tsawon watanni 6 inji wani jamiinMajalisar Dinkin Duniya, ko MDD.