Zaben Fatoumata Tambajang ya zo ne a daidai lokacin da Barrow ke cigaba da shirin komawa Gambiya daga makwabciyar kasar Senegal, inda aka rantsar da shi shugaban kasa cikin makon da ya gabata a lokacin da Jammeh ya ki sauka daga karagar mulki.
Jammeh ya bar Gambiya ranar Asabar din da ta gabata bisa barazanar daukar matakin soja da kungiyar kasashen ECOWAS tayi. Da, tsohon shugaban ya ki ya amince da nasarar da Barrow ya samu a zaben da ka yi ranar 1 ga watan Disambar bara.
A wata hira da Muryar Amurka tayi da shugaba Barrow shekaranjiya Lahadi, ya ce zai kafa wani kwamitin sasanchi wanda zai binciki zargin saba dokokin shugabanci a cikin shekaru 22 da Jammeh ya kwashe yana mulkin kasar.
Wani mai ba shugaba Barrow shawara ya fadawa manema labarai jiya litinin cewa, kafin Jammeh ya bar kasar ranar Asabar, ya sace kudi dala miliyan 11 daga asusun gwamnati ya kuma fitar da motoci masu tsada daga kasar ta jirgin sama. Dama kungiyoyin raji sun zarge shi da saba hakkokin bil’adama a lokacin mulkinsa, ciki har da daure abokan adawa da ‘yan jarida a gidan wakafi.