Wannan jawabin nasa na zuwa ne bayan da ya yi jawabi ga Kwamitin Sulhu na MDD jiya Laraba game da halin da ake ciki a kasar.
A wata hirar da ya yi da Muryar Amurka, Ibn Chambas ya ce akwai bukatar tabbatar da tsaron lafiyar Shugaba Barrow, da gwamnatinsa da ke tafe da kuma uwa-uba 'yan kasar ta Gambia.
"Ya kamata mu ba da goyon bayanmu don su tabbatar da gwamnatin ta dora daga inda ta da ta tsaya; mu kuma fahimci yadda aka tsara mika mulkin saboda abin ya gudana ba tara da wata tangarda ba. Wannan al'amarin ya zarce batun wani Yahaya Jammeh. Yanzu ba ta shi ake ba. A yanzu tambayar ita ce: yaya za a yi mulkin; yaya tsarin gwamnatin zai kasance; yaya za a tsara wadannan abubuwa? MDD dai ta zaburo. Tuni muka tura wani kwararre kan harkar mika mulki cikin lalama wanda zai taimaka," a cewar Ibn Chambas.