Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya fada a babban taron majalisar cewa, nasara na kokarin sabule wa duniya a yakin da ake yi da matsalar sauyin yanayi, amma a cewar shi, har yanzu akwai sauran lokacin da za a dakile mummunan tasirin da dumamar yanayi ke yi ga duniya.
Ya kara da cewa, a ranar Litinin, an tattauna kan wannan batu a wani taron koli, inda ya yi kira ga shugabannin duniya da su himmatu wajen ganin an samar da maslahar da za ta tsayar da yanayi a maki daya da rabi, sannan a kai shallin samar da daidaito game da gurbatacciyar iskar da ake fitarwa nan da shekarar 2050.
Shi dai Guterres, na daya daga cikin shugabannin duniya cikin jerin shugabannin kasashe da suka yi jawabi a ranar farko ta taron koli kan batun sauyin yanayi da ya shafi duniya baki daya.
Facebook Forum