Wani kwamitin kwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da wani rahoto kan makomar duniyarmu mai nuna cewa wani babban bala'i na tafe muddun ba a rage dumamar yanayi ba.
Kwamitin na bai daya na kasashen duniya kan yanayi ya zaiyana a rahoton nasa yadda yanayin duniya da sha'anin lafiya da kuma rayuwar halittun cikin ruwa duk za su kasance cikin matukar hadari muddun shugabannin kasashen duniya ba su dau matakin ganin dan adam ya rage dumama yanayi zuwa zafi mai yawan Fahrenheit 9 tsakanin 2030 zuwa 2052 ba, a maimakon abin da aka tsai da shawara a kai na zafin Fahrenheit 1.8 a baya.
Wasu daga cikin alfanun takaita dumamar yanayi kasa da yadda aka tsaida ada sun hada da cewa: yawam mutanen da za su yi fama da karancin ruwa zai ragu da rabi; yawan wadanda za su mutu sanadiyyar zafi da cututtuka masu yado shi ma zai ragu.
Ta kuma yiwu hamadar kankarar nan ta Yammacin Antartic ta daina narkewar da ta ke yi dinnan babu kakkautawa. Kuma hakan zai iya taimakawa wajen ceto akasarin kananan halittun ruwa masu kama da tsirai din nan daga mutuwa.
Facebook Forum