Sojojin kasar Kenya su na fuskantar matsalolin ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma laka da tabo kan hanyoyi, a yayin da suka kutsa cikin yankuna akalla biyu na Somaliya makwabciyarsu domin farauto ‘ya’yan kungiyar kishin Islama ta al-Shabab.
An ce a yanzu haka sojojin Kenya su na kusa da garin Afmadow dake hannun al-Shabab a yankin Jubba na Somaliya, inda aka ce mazauna su na ta gudu domin tsoron kada a rutsa da su a fadan da ake ji za a gwabza.
Jami’ai da shaidu sun fadawa Muryar Amurka jiya talata cewa sojojin Kenya, tare da jiragen yakinsu na helkwafta, sun shige ta garin El-Waq dake bakin iyaka suka shiga cikin yankin Gedo na Somaliya.
Jiya talata a babban birnin na Somaliya, watau Mogadishu, jami’an gwamnatin Kenya da na Somaliya sun yi alkawarin daukar matakan rigakafin hare-hare a kan kungiyoyi masu makamai dake barazana ga kasashen biyu. Da alamun yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma ta takaita matakan sojan da kasar Kenya zata iya dauka a cikin yankin Jubba ta kasa kawai.