Wasu mata biyu za su gurfana a gaban shari’a a jahar Minnesota a nan Amurka bisa zargin su da taimakawa kungiyar mayakan al-Shabab ta kasar Somaliya da tattara mu su kudi da kuma daukar mu su sabbin mayaka.
Matan wadanda dukan su biyu, Amurkawa ne, ‘yan tsatson kasar Somaliya, su na fuskantar dimbin tuhume-tuhume a shari’ar da za a fara yi mu su a yau litinin.
Lauyoyin gwamnati masu shigar da kara sun ce Amina Farah Ali ‘yar shekaru 35 da kuma Hawo Mohamed Hassan ‘yar shekaru 64 sun karbi kudade a wurin ‘yan kasar Somaliya mazauna jahar Minnesota su ka aikawa kungiyar al-Shabab mai dangantaka da al-Qaida.
Gwamnatin kasar Amurka ta ce watannin goma ta yi, ta na satar sauraren hirar Amina Farah Ali ta wayar gidan ta, da kuma wayar ta, ta hannu, gwamnatin ta ce ta saurari hirarrakin ta kimanin dubu 30. Haka kuma a cikin wasu bayanan kotu an rubuta cewa masu bincike sun duba sharar gidan Amina Farah Ali sau fiye da a kirga.
Matan biyu sun ce sun bukaci taimakon kudi daga ‘yan kasar Somaliya mazauna jahar Minnesota ne da niyyar yin ayyukan lada. Amma masu shigar da kara sun ce an yi amfani da kudaden ne wajen taimakawa wasu mutane 20 a kalla su tashi daga Minnesota zuwa Somaliya su shiga kungiyar mayakan al-Shabab.
Amina Farah Ali da Hawo Mohammed Hassan na fuskantar zargin hadin bakin samar da taimako ga wata kungiyar ‘yan ta’addan wata kasar waje. Amina Farah Ali na fuskantar tuhumce-tuhumcen aikata karin wasu laifuffuka 12 bisa zargin ta da turawa kungiyar al-Shabab kudi fiye da dola dubu 8 da 600 a farkon shekarar dubu biyu da takwas.
Matan na cikin wasu mutane 20 da ake zargi da hannu cikin wani shirin taimakawa kungiyar ta al-Shabab. Wasun su, sun amsa laifi, a yayin da wasu ke zaman jiran shari’a wasu kuma su ka gudu.