Kwamitin Sulhun MDD na shirin duba yiwuwar daukan sabbin matakan ladabtar da kasar Eritrea bisa zargin ta da neman tada zaune tsaye a kasashen da ke makwaftaka da ita.
A yau talata kwamitin Sulhun mai wakilai 15, ya kamata ya fara tattauna shawarwarin haramta zuba jari a masana’antar hakar ma’adinan kasar Eritrea, sannan ya kara daukan wasu matakan haramta yin balaguro ga shugabannin kasar kuma a kama kadarorin su da ke kasashen waje.
A shekarar dubu biyu da 9 kwamitin sulhun ya kafa dokar haramta cinikin makamai da Eritrea, da kuma daukan matakan takurawa wasu shugbannin kasar saboda zargin da aka yiwa kasar cewa tan a tallafawa ‘yan gwagwarmayar Islamar kasar Somaliya.
Kwanan nan sashen MDD mai lura da karfafa matakan ladabtarwar a kan kasar Eritrea, ya fada cewa Eritrea ce ta shirya wata makarkashiyar neman farfasa boma-bomai a wurin taron kolin kungiyar kasashen Afirka a Ethiopia a cikin watan janairun da ya gabata.
Eritrea ta musanta zargin cewa ta na goyon bayan ‘yan tawayen kasar Somaliya, kuma ta musanta cewa ta na da hannu a cikin makarkashiyar neman kai harin bom din, sannan kuma ta yi kira ga kwamitin sulhun MDD cewa ya cire dukkanin matakan ladabtarwar da ya dauka a kan kasar.
Eritrea ta dora laifin yin kaimin daukan matakan a kan abokiyar gabar ta Ethiopia, wadda su ka yi shekaru biyu su na fafata yakin kan iyaka , daga shekarar 1998 zuwa shekarar dubu biyu.