To amma bisa ga wasu alamu gwamnonin arewacin Najeriya sun kama turban ingantawa da kuma farfado da matakan ilimi a jihohinsu ta hanyar gina sabbin makarantu da kuma gyara tsofofin. Suna kuma daukan sabbin kwararrun malamai tare da samar ma daliban da malaman isassun kayan aiki.
Misali a makarantar sakandaren gwamnati ta 'yammata GSS Doma a jihar Gombe an mayar da ita sabuwa fil. Wasu daga cikin daliban sun godewa gwamnatin Ibrahim Dankwambo da gyaran da aka yi masu da basu isassun malamai da kayan aiki. Gyaran bai tsaya kan gidajen makarantar ba har da ma inganta irin abincin da ake basu. Daliban sun ce da basa samun malamai. Wasu ranakun ma sai su zauna cikin azuzuwansu daga safe har karshen wa'adi babu wani malamin da zai shigo ya koya masu. Yanzu ba haka lamarin yake ba. Malamai na zuwa koyas da su kan lokaci.
A nashi kalamun Gwamnan Gombe Alhaji Ibrahim Dankwambo ya yi karin bayani kan wannan batun. Ya ce duk wanda aka bashi ilimi an bashi jari. Ya ce idan sun samu sun ba mutum ilimi to sun samar masa hanya ta rayuwa ta din-din-din. Ya ce kawo yanzu gwamnati ta dauki malamai dake koyaswa a firamare dubu daya. Haka ma a sakandare an dauki malamai dubu daya. Yace yadda suke yiwa makarantu kwaskwarima haka suke kara inganta matsayinsu. Yadda ake gyara makarantun maza haka ake gyara na mata. Gwamnan ya yi misali da makarantar 'yammata ta Doma inda yanzu akwai 'yammata kimanin dubu biyar suna karatu.
Hatta makarantar da aka yi domin daliban wasu jihohin an gyarata an kuma kayatar da ita. Gwamnan ya ce kuma gwamnati ke biyan kudin jarabawar duk wani dalibi ko gada ina ya fito. Alhaji Adamu Babawuro kakakin kungiyar iyaye da malaman makarantar jihar Gombe ya yaba da yunkurin da gwamnan ya yi. Ya ce ya gani da idanunsa. An gyara tsoffin makarantu an kuma gina sabbi. Ya ce da ana koyaswa a karkashin bishiyoyi to amma yanzu kowane dalibi na daukar karatu a cikin aji.
Ga rahoton Abdulwahab Mohammed.