DIFFA, NIGER - Akasari dai mazauna garuruwan da suka hada Toumour da Kabalewa da kuma Gingime ne ke gudun hijira daga garuruwan nasu na asali zuwa birnin na Diffa sakamakon yadda wannan al’amarin sace-sacen mutane domin neman kudin fansa dama hallaka mutane ke kara ta’azzara.
Ga dukkanin alamu wannan al’amarin zai iya mayar da hannun agogo baya a kokarin da hukumomin Nijar suke yi na ganin sun mayar da ‘yan gudu hijira na garuruwan jihar ta Diffa kimanin 45 a garuruwansu na asali bayan kusan shekaru takwas suna gudun hijira a birnin na Diffa sakamakon rikicin ‘yan kungiyar Boko Haram.
A cewar mai fashin baki na al’ummuran yau da kullum a jihar ta Diffa Ibrahim Maman wannan sabon gudun hijirar yafi na baya illa idan aka yi la’akari da halin da ‘yan gudu hijra suke ciki a wannan lokaci.
Sai dai a cewar mataimakin shugaban Majalisar Mashawartan Jihar Diffa Arimi Mustapha wannan sabon gudun hijirar ba zai kawowa gwamnatin cikas ba akokarin nata na mayar da wadannan ‘yan gudun hijirar a garuruwansu na asali, domin tuni wasu mazauna garuruwa takwas suka koma garuruwansu na asali ba tare da hannun hukumomin ba.