Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hatsarin Kwale-Kwale A Delta Ya Hallaka Mutane 5 A Delta


Hadarin Kwale Kwale Jihar Kirfi
Hadarin Kwale Kwale Jihar Kirfi

Mutane 5 sun mutu, 6 sun jikkata sannan wasu 20 sun bata sakamakon wani mummunan hatsarin kwale-kwale daya afku a karamar hukumar Warri ta kudu a jihar Delta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta Edafe Bright ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya bayyana cewar mutane 6 da suka jikkata na samun kulawar likitoci a wani asibitin da ba’a bayyana ba a birnin Warri.

Mummunan hatsarin ya kunshi taho mu gama tsakanin wasu kananan jiragen ruwa masu gudun tsiya guda 2 dake fiton wasu iyalai dake dawowa daga bikin jana’iza.

A watan Oktoban daya gabata, dimbin mutane sun mutu a jihar Neja bayan da wani kwale-kwale ya kife saboda kazamin lodi. Kwale-kwalen na dauke ne da fiye da fasinjoji 300 sa’ilin daya kife a kogin Gbajibo dake karamar hukumar Mokwa ta jihar.

Kwale-kwalen ya taso ne daga garin Mundi zuwa Gbajibo bayan halartar bikin Maulidi sa’ilin da hatsarin ya afku.

Makamancin wannan hatsari ya faru a jihar a watan Satumbar 2023 sa’ilin da wani kwale-kwalen dake dauke da fasinjoji 50 ya kife, inda ya hallaka mutane 24 dake kan hanyarsu ta zuwa gona domin girbi.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG