Malam Yazid Bala Alhassan, shine jami’in dake kula da gidan kason dake jihar Kaduna, kuma ya bayyana dalilan dake kawo cunkoso a gidan kaso wadanda suka hada da neman abinci, domin a cewarsa ana ciyar da ‘yan hursuna sau uku a rana lamarin da ya sa wasu da dama sun garace su zauna a gidan yari.
Da yake amsa tambayar da wakilin sahsen Hausa na muryar Amurka Isa Lawal Ikara, ya yi masa akan masu kananan laifin da ake kaiwa gidan kaso ba tare da an sallami wasu ba, shugaban ya bayyana cewa basu da irin wadannan a gidajen yarinsu domin kuwa gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti karkashin kulawar kwamishinan shari’a domin ziyartar gidan yari komai kankantar sa domin rage masu kananan laifuka.
Malam Yazid ya kara da cewa duk da kokarin rage masu kananan laifukan da kwamitin ke yi, har yanzu gidajen kason a cunkushe uke da jama’a sakamakon yawan aikata laifukan da ake, sa’an nan akwai hanyoyin horas da mai laifi kamar su cin tara kokuma zuwa shara a kasuwa da sauransu, duk hanyoyi ne na rage yawan cunkoso a gidajen yari.
Ya kuma kar da cewa wata hanya ta rage wannan matsala ita ce samawa matasa ayyukanyi domin rashin ayyukan yin a daga cikin dalilan da ke sa matasa aikata laifuka, misali wadanda suka koyi sana’ar hannu kamar su aski, gyaran gashi da kwamfuta, da zarar an sallame su daga gidan kaso basa sake komawa.
Barista Muhammad Ibrahim Zaria, masanin shari’a ne kuma lauya ne mai zaman kansa ya bayyana cewa da dama da ya kamata a yi masu shari’a anyi watsi da su, wasu kuma basu da kudin beli.
Domin Karin bayani saurari rahoton Isa Lawal Ikara.
Facebook Forum