Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Alhaji Yakubu Bello na jihar Oyo, ne ya bayyana hakan jim kadan da ya kai wata ziyara a fadar sarkin kisi a jihar Oyo, Oba Mosud Oyekola Aweda Lawal, tare da jama’arsa.
Alhaji Yakubu Bello, ya ce sun dauki wannan mataki ne don samar da zaman lafiya a tsakanin makiyaya da manoma, har wa yau ya kara da cewa an hana wa makiyaya su dauki babbar bindiga samfurin ak 47 a lokacin kiwo sai dai bindiga harba-ka-ruga, ya kara da cewa wanda aka kama da ak 47 baya cikin kungiya kuma gwanati ta dauki matakin hukunta shi.
Shugaban ya bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne a sakamakon tabbatar da dauwamammen zaman lafiya a tsakanin makiyaya da daukacin jama’ar al’umma domin a cewar sa kiwon dare na daga cikin dalilan dake haddaa fitinar dake shafar wadanda basu ji ba basu gani ba.
Alhaji Muhammadu Mufure, shine aka nada shugaban kungiyar Miyetti Allah, a karkashin karamar hukumar Erekpo, ta jihar Oyo, kuma ya sha alwashin tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.
Shugana makiyaya na karamar hukumar ya bada goyon bayansa tare da yin kira ga dukkan bangarorin.
Daga Ibadan ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.
Facebook Forum