Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Uku a Jihar Filato


Gwamnan Jihar Filato Mr. Simon Lalon
Gwamnan Jihar Filato Mr. Simon Lalon

Harin da wasu ‘yan bindiga ya rutsa da mutane uku a kauyen Were dake cikin karamar hukumar Barkin Ladi da suka hada da tsohon shugaban ma’aikatan jihar da wani jami’in soji

Rundunar tsaro ta jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane uku yayinda wasu suka samu raunuka a wani harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Were cikin karamar hukumar Barkin Ladi.

Wasu da ba’a tantance ba ne suka kai harin da daren Talata inda suka hallaka mutane uku cikinsu har da jami’in soja daya da kuma tsohon shugaban ma’aikatan jihar Filato.

Kakakin rundunar tsaron jihar, Kyaftin Umar Adam, ya bayyanawa wakiliyarmu dake Jos, Zainab Babaji yadda lamarin ya auku.

Kyaftin Adam yace a wani shago ne lamarin ya auku, inda wasu mutane biyu da suka je sayayya a wurin tare da wata mai sayar da kayan a shagon suka hallaka. Wadanda suka isa wurin domin taimakawa su ma an ji masu ciwo.

Yanzu dai sojoji da ‘yansanda suna sintiri a wurin tare da yin bincike domin su gano wadanda suka aikata ta’asar.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG