Wakilinmu a jihar Borno Haruna Dauda ya ce dama Shugaban kasa ke da ikon kafa dokar bisa amincewa ‘yan Majalisar Tarayya. Ya ce dayake bayan cikar wa’adin an kara shi bisa bukatar Shugaban kasa da kuma amincewar ‘yan Majalisar Tarayya – gashi kuma dokar ta hada da katse layukan salula, wanda hakan ya janyo gurgunda sana’o’i da sadarwa da walwalar jama’a a jihar Borno, ‘yan jihar sun shiga kokawa sosai ganin za su sake kasancewa cikin rashin layukan sadarwa na wani wa’adin tsawon wata shida.
Honorabul Muhammed Banga, Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dokokin jihar ta Borno, ya yi takaicin yadda za a sake kwashe wani tsawon lokaci ba layukan sadarwa a jihar bayan kuwa, in ji shi har an dan sami kwanciyar hankali a wasu sassan jihar.
Shi ma wani dan kasuwa mai suna Baba Kaci ya koka cewa rashin layukan sadarwa ya janyo koma baya ga harkar kasuwanci. Haka shi ma wani mai sayar da kayan gwari mai suna Abba Bulama ya jaddada.