Inji Nick Dazan abun takaici ne a ce jama'iyya irin Republican bata samu wani dan takaran da zai tsaya mata ba sai Donald Trump wanda kalamunsa na harzuka jama'a ne.
Yace jam'iyyar Republican ce ta samar da shuganni irin su Fraklin D Rosevelt, Ronald Reagan da su Bush da suka shugabanci kasar tare da yin gagarumin aiki da kawo cigaban kasar. Duk wadannan natsatsun mutane ne amma sai gashi an wayi gari an samu wani wanda zai sawa dimokradiya illa.
Yace kodayake a Najeriya dimokradiya jaririya ce koyo kuma su keyi amma idan sun ga abun da ba daidai ba dole su kauce masa. Su ba zasu yi koyi da abubuwan da Donald Trump ya keyi ba ta wajen kalamai da nuna kyama ga wasu da ingiza mutane har da ma tsoratar da mutane.
Nick Dazan yace duk wani mutum da zai sa mutane cikin zullumi bai kamata a ce shi ne ma zai yi shugabanci ba. Donald Trump ya baudewa siyasar akida ya kawo wasu abubuwa daban. Abun da yakamata shugaba ya damu dasu su ne yadda za'a yi zamantakewa da yadda za'a inganta rayuwar jama'a da yadda za'a yi zaman lumana.
Irin Trump bai kamata ya rike iko da karfin da Amurka ke dashi ba saboda zai yiwa kananan kasashe barazana.
Ga firar Nasiru El-Hikaya da karin bayani.