Yayinda aka ba Modu Sheriff shugabancin jam'iyyar watanni ukku ya kamata yayi domin ya kammala wa'adin yankin arewa maso gabas kana ya shirya zaben da zai fitar da shugaba amma bai yi hakan ba.
Idan har jam'iyyar ta kasa warware rikicin da ta fada ciki yanzu ta hanyar lumana wasu na ganin wani bangare na iya hada kai da wasu jam'iyyun domin kafa wata daban.
Alhaji Adamu Maina Waziri wani jigon jama'iyyar kuma tsohon ministan harkokin 'yansanda a zamanin mulkin Obasanjo yace a matsayinsu na mutanen yankin arewa maso gbas inda Ali Modu Sheriff ya fito suna kira gareshi ya daina abun da ya keyi. Yace ya isa haka nan. Tunda wa'adinshi ya kare ya sauka. Yace taronsu shi ne zai nuna masa cewa a gida ma sun kalubalanceshi bisa abun da ya keyi.
Bisa tsarin jam'iyyarsu Alhaji Waziri yace uwar jam'iyya ta ba Ahmadu Makarfi izinin ya yi shugabanci na wucin gadi kana ya shirya taron da zai fitar da sabbin shugabanni saboda haka Modu Sheriff dole ne ya kau.
Sanata Abdul Ningi daya daga cikin mamban kwamitin riko da jam'iyyar ta kafa yace tabbas rikicin PDP ya samo asali ne daga shiyar arewa maso gabas, wato yakinsu. Yace yankinsu aka ba shugabanci na shekara hudu. Saura watanni ukku su kammala aka dauko Modu Sheriff ya cika watanni ukkun domin a yi zabe.
Hajiya Zainab Maina tsohuwar minista kuma shugabar mata kuma 'yar kwamitin amintattun jam'iyyar tace sun zo taron tattaunawa ne domin su gayawa kansu gaskiya kan dalilan da suka sa jam'iyyar ta fadi zaben 2015.
Shi ma Alhaji Shehu Musa Gaban daya daga cikin wadanda suka kafa PDP tun farkonta yace makasudin taron shi ne fito da hanyar da zasu gyara jam'iyyar.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.