Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rudani Ya Biyo Bayan Zaben Gwamnan Kogi


INEC
INEC

Bayan rasuwar dan takarar jam'iyyar APC Prince Abubakar Audu hukumar zabe ko INEC ta nemi jam'iyyar da ta maye gurbin marigayin.

Jam'iyyar dai ta tsayar da Alhaji Yahaya Bello maimakon James Faleke wanda shi ne mataimakin Prince Abubakar Audu wanda Allah ya yiwa rasuwa.

To amma shi James Faleke ya yi watsi da matakin da jam'iyyarsa ta dauka kuma tuni ya garzaya kotu. Ya nemi babban kotun tarayya dake Abuja ta ayyanashi a matsayin gwamnan Kogi.

Masana harkokin shari'a sun yi tsokaci akan matsayin mataimakin gwamna. Mr. Oluwole Osaze Ozu daraktan wayar da kawunan masu kada kuri'a a hedkwatar hukumar zaben Najeriya a idonsa da ma idon APC James Faleke shi ne zababben mataimakin gwamnan jihar Kogi. Yanzu dai shi Faleke yana shirye-shiryen yadda kotu zata tabbatar da shi a matsayin gwamnan jihar.

Barrister Aliyu Abdullahi yace a idon doka Faleke shi ne mataimakin gwamna kuma tunda babu gwamna shi ne yakama ya zama gwamna.Amma Barrister Mainasara Kogo Ibrahim yace a yi taka tsantsan. Yace idan tayi zafi kotu na iya soke zaben APC gaba daya ta ba jam'iyya da ta fi yawan kuri'u wadda kuma take da tsayayyen dan takarar kujerar, wato a nan PDP ke nan.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG