Jam'iyyar ta tsayar da Alhaji Yahaya Bello a matsayin wanda zai maye gurbin marigayi Abubakar Audu a zaben jihar Kogi da za'a kammala a karshen wannan makon.
Bayan shugabannin APC sun yi doguwar tattaunawa daga bisani sun yanke shawarar tsayar da Alhaji Bello wanda a zaben fitar da gwani da aka yi kafin zaben ya zo na biyu yayinda Abubakar Audu ya zo na daya.
Suleiman Abdulmalik jigo a jam'iyyar reshen Kogi kuma sakataren yada labarai na marigayi Abubakar Audu yana cikin shugabannin APC da suka halarci zaman na Abuja inda aka yanke shawarar tsayar da Alhaji Bello.
Yace babu abun da zasu ce sai dai su bi umurnin uwar jam'iyyar. To saidai James Faleke wanda ya tsaya a mataimakin Abubakar Audu ya turje sai a bashi ya maye gurbin wanda suka tsaya takara tare a karkashin jam'iyyarsu.
A wani gefen kuma jam'iyyar PDP ta ja daga inda tace maganar zaben cike gurbi bai taso ba saidai a mikawa nata dantakarar kujerar..Ndagi Abubakar na PDP yace babu maganar zabe saidai a ba wanda yake raye kujerar saboda wai kuri'un matace su ma matattu ne.
Wani masanin shari'a Barrister Abdulmalik Sarkin Daji yace matsayin na PDP abu ne mai daure kai a dokance.
Ga karin bayani.