Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kogi: Sabon Gwamnan Jihar Na Fuskantar Turjiya daga Jam'iyyarsa da PDP


Shugaban INEC Mahmud Yakubu
Shugaban INEC Mahmud Yakubu

Bayan da INEC ta bayyana Alhaji Yahaya Bello a matsayin sabon zababben gwamnan jihar Kogi, yanzu gwamnan yana fuskantar turjiya daga jam'iyyarsa musamman masu goyon bayan mataimakinsa da kuma jam'iyyar PDP

Yanzu dai tana kasa tana dabo a jihar Kogi biyo bayan bayyana Yahaya Bello na jam'iyyar APC a matsayin sabon gwamnan jihar da hukumar zabe ta INEC ta yi.

Shi dai Alhaji Yahaya Bello ya gaji Abubakar Audu ne wanda ya rasu tun kafin a kammala zaben. To saida sabon gwamnan na fuskantar turjiya daga bangarori guda biyu.

Masu goyon bayan mataimakin marigayin James Faleke sun hau kujerar naki, suna ganin mataimakin ya kamata ya gaji Abubakar Audu. Haka ma bangaren Idris Wada na jam'iyyar PDP ya ki amincewa da Yahaya Bello. Dukansu suna damarar zuwa kotu.

PDP dai tana neman a ruguza zaben kana a sake lale. Tsohon shugaban karamar hukumar Lokoja na bangaren Faleke a jam'iyyar APC yace tunda uwar jam'iyyar ta yi masu karar tsaye dole wani abu ya biyo baya.

Su ma a bangaren PDP suna neman a baiwa Idris Wada kai tsaye tunda abokin takararsa ya riga ya rasu. Suleiman Babadoko jigo a jam'iyyar PDP a jihar yace Idris Wada ne ya zo na biyu saboda haka kamata ya yi a bashi.

Duk da turjiyar da sabon gwamnan ke fuskanta talakawan jihar na fatan sabon gwamnan zai kula dasu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG