Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ronaldo Na Fama Da Rashin Lafiya


Cristiano Ronaldo a kwance yana samun kulawa a wata karawa da suka yi da kasar Czech a gasar Nations League ta UEFA (AP Photo/Petr David Josek)
Cristiano Ronaldo a kwance yana samun kulawa a wata karawa da suka yi da kasar Czech a gasar Nations League ta UEFA (AP Photo/Petr David Josek)

Tawagar Portugal za ta kara da Najeriya a ranar Alhamis a wasan sada zumunta a Lisbon, daga bisani kuma sai ta nausa zuwa Qatar inda za ta fafata a gasar cin kofin duniya.

Cristiano Ronaldo bai yi atisaye da tawagar ‘yan wasan kasarsa ta Portugal ba a ranar Laraba, saboda yana fama da ciwon ciki a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Wannan rashin lafiya ya sa dan wasan na Portugal ba zai samu damar buga wasan ta da tsimi da kasar ta Portugal za ta yi da Najeriya ba.

Tawagar Portugal za ta kara da Najeriya a ranar Alhamis a Lisbon daga bisani kuma sai ta nausa zuwa Qatar domin karawa a gasar cin kofin duniya.

Mai horar da ‘yan wasan Portugal Fernando Santos ya ba da tabbacin cewa Ronaldo ba zai kara a wasan da Najeriya ba.

Najeriya dai ba ta samu gurbin zuwa gasar ba bayan da Ghana ta fidda ita a wasannin nema shiga gasar.

Wannan lamari na faruwa ne bayan bullar wani sashi na wata hira da ya yi da wani gidan talabijin, inda ya caccaki kungiyarsa ta Manchester United.

Cikin hirar Ronaldo ya ce kungiyar ta United “ta ci amanarsa,” sannan ba ya ganin mutuncin kocin kungiyar Erik ten Hag.

United ta ce za ta mayar masa da martani idan ta kammala bincikenta.

Portugal wacce ke rukuni H za ta fara karawa ne da Ghana a ranar 24 ga watan Nuwamba.

Rukunin na H har ila yau na dauke da Uruguay da Koriya ta Kudu.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG