A karshe dai kungiyar kwallon kafar Manchester United ta Ingila ta yanke shawarar sayar da shahararren dan wasanta Cristiano Ronaldo, kwana daya bayan mummunan kashin da ta sha a hannun Bournmouth da ci 4-0, a mako na 2 na gasar Premier a ranar Asabar.
Tun a watan jiya ne Ronaldo ya bayyana wa kungiyar bukatarsa ta sauya wurin taka leda, musamman domin fafata gasar zakarun Turai, a yayin da United din ba ta da gurbin gasar a wannan kakar wasanni.
Duk da yake a can farko wasu manyan kungiyoyi kamar Chelsea sun nuna sha’awa ga dan wasan, amma kuma sabon kocin kungiyar Eric Ten Hag, ya dage kan cewa Ronaldo ba na sayarwa ba ne, domin kuwa yana a cikin sabon tsarin da ya zo da shi na farfado da kungiyar.
To sai dai kuma duk da yake an fi danganta Ronaldo da komawa Chelsea din, wasu rahotanni sun bayyana cewa United ba ta bukatar dan wasan ya koma wata kungiya da suke adawa a ita, dalili ke nan da ya sa a yanzu ma suka yanke shawarar sayar da shi kadai ga kungiyar Atletico Madrid ta kasar Spain.
An kuma ruwaito cewa ita kan ta Atletiko din tana bukace da Ronaldo, domin cike gibin da shahararren dan wasanta Luis Suarez ya bari.
A Ingila din kuma dubun dubatar magoya bayan kungiyar Chelsea ne suka rattaba hannu a wata takardar koke, da ke neman hukumar shirya gasar Premier ta haramta wa alkalin wasa Anthony Tailor alkalancin kowane wasa da kungiyar za ta buga nan gaba.
Magoya bayan Chelsea din na bayyana bacin rai ne kan abin da suka kira rashin adalcin da alkalin wasan yayi, a lokacin wasan da kungiyar ta yi kunnen doki da ci 2-2 da Tottenham a gasar Premier a jiya Lahadi.
Da dama daga cikinsu sun ce sun dade suna bibiyar alkalancin wasan Chelsea da Taylor ya yi, inda kuma suke ganin kamar yana da wata boyayyiyar manufa ne kan kungiyar.
Wasan dai ya yi zafin gaske ta yadda a karshe ma aka sami takun saka tsakanin masu horar da ‘yan wasan kungiyoyin 2, wanda ya kai ga ba su jan katin kora, da zai haramta musu shigowa fili na tsawon wasanni 3-3.
To sai dai a ra’ayin mai sharhi kan lamurran wasanni, Umar Faruk Bukkuyum, wannan ba abin mamaki ba ne.
Shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFF, Amaju Pinnick ya bayyana cewa bai da sha’awar sake tsayawa takarar shugabancin hukumar karo na 3, idan wa’adin mulkinsa na 2 ya kai karshe.
Pinnick wanda tsohon shugaban hukumar kwallon kafar jihar Delta ne, ya dare kan kujerar shugabancin NFF din ne sa'adda aka zabe shi a shekara ta 2014, kana kuma aka sake zabensa a wa’adin mulki na 2 a shekarar 2018, wadda za ta karkare a wannan shekara ta 2022.
A can baya an sami rade-radin cewa Pinnick, wanda yana cikin ‘yan kwamitin zartarwa na hukumar kwallon duniya ta FIFA, yana da sha’awar sake tsayawa takara karo na 3.
Saurari cikakken rahoton Murtala Faruk Sanyinna: