Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsare Dadadden Shugaban Kasar Zimbabwe a Gidansa


Sojoji da tankunan yaki sun rufe hanyar da ta tafi gidan shugaba Robert Mugabe
Sojoji da tankunan yaki sun rufe hanyar da ta tafi gidan shugaba Robert Mugabe

Biyo bayan abun da sojojin Zimbabwe suka yi jiya da yayi kama da juyin mulki, yanzu dai tsohon shugaban kasar Robert Mugabe yana tsare a gidansa inji sojojin sai babu wani tabbas inda yake takamaimai

An tsare dadadden Shugaban kasar Zimbabwe a gidansa, a cewar Shugaban Afirka Ta Kudu a jiya Laraba, al’amarin da ke cigaba da jefa makomar Robert Mogabe cikin duhu, bayan al’amarin nan da ke dada yin kama da wani yunkuri mai samun goyon bayan soji na hambarar da shi bayan tsawon shekaru 37 bisa gadon mulki.

Kafafen sada zumunci na nuna cewa ana zaman dardar a Harare, babban birnin kasar, yayin da wasu wuraren kasuwanci ke saurin rufewa.

Kasar da ta taba yi ma Zimbabwe mulkin mallaka, Ingila; ta yi kiran da a kai zuciya nesa bayan wani al’amarin da, ga dukkan alamu, juyin mulki ne aka yi ma Shugaban kasar, Robert Mugabe.

Tun da sanyin safiyar jiya Laraba ‘yan adawa suka fara shagulgula a ofishin jakadancin Zimbabwe da ke birnin London, ganin alamun gwamnatin Robert Mugabe ta zo karshe.

“Lallai mu jinjina ma kanmu kan abubuwan da mu ka yi gabanin nan. To amma kash; mun kasa daukar matakin da ya dace, tun a lokacin da ya kamata ace ya sauka. Tun da dadewa ya kamata ya sauka,” a cewar Chipo Parirenyatwa na kungiyar rajin kare hakkin dana dam shiyyar Zimbabbwe ga Muryar Amurka.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG