Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Zimbabwe, Sojoji Sun Hambare Gwamnatin Robert Mugabe.


Wani sojan Zimbabwe yake tafiya tasakiyar birnin Harare.
Wani sojan Zimbabwe yake tafiya tasakiyar birnin Harare.

Kakakin mayakan kasar SB Moyo, yace matakin kakkabe zarmiya ne a tafarkin siyasar kasar.

Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma yace, an yiwa Robert Mugabe shugaban Zimbabwe "daurin talala" a wani mataki da sojojin kasar suka dauka na hambare gwamnatin Mugabe wanda yayi shekaru 37 yana mulkin kasar.

Shugaba Zuma, wanda shine shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen dake kudancin Afirka da ake kira (SADC a takaice, ya fada cikin wata sanarwa cewa, yayi magana da shugaba Mugabe da safiyar Laraban nan, wanda ya tabbatar "cewa an yi masa daurin talala, amma yace lafiyarsa lau." Haka nan Zuma yace, Afirka takudun tana magana da rundunar mayakan kasar ta Zimbabwe."
Matakin, babu mamaki martani ne kan yunkurin da bashi da farin jini da shugaba Mugabe ya fara dauka a farkon watan nan, inda ya kori mataimkainsa, Emmerson Mnangagwa, kuma ya nuna misalin yana son ya maye gurbin Emeerson da uwargidansa.

A jiya Talata, tankunan yaki suka mirgina kan titunan Harare babban birnin kasar, kwana daya bayan da babban hafsan sojojin kasar, Janar Constantino Chiwenga, yayi gargadin cewa "zai dauki mataki" sai har Mugabe ya tsaida kakkabe magoya bayan Emeerson a jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar.
Sojoji sun kama tashar talabijin ta kasar a safiyar Laraban nan.

"Muna so mu fito karara mu bayyana cewa, wannan ba juyin mulkin soja bane," inji kakakin runduar sojin kasar Manjo Janar SB Moyo. Ya ci gaba da cewa, abunda dakarun Zimbabwe suke yi shine, taka birki ga tabarbarewar harkokin siyasa, dana zamantakewa da ci gaban tattalin arziki a kasar mu, wadda idan ba'a tunkare shi ba, zai kai ga mummunar zubda jini."

Jam'iyyar ta ZANU-PF mai mulkin kasar ta fada a shafinta a internet cewa, tsohon mataimakin shugaban kasar Mnangagwa zai koma kasar. Yanzu dai ba'a san inda yake ba, kodashike akwai rade-raden cewa yana Afirka ta kudu.

Shaidun gani da ido suka ce sun ji akalla fashe fashe daban daban har uku, da tashin bindigogi a safiyar yau Laraba, a Harare babban birnin kasar.

A daren jiya talata, an ci zarafin wakilin Muriyar Amurka wanda yayi kokarin daukar labarai a kafar yada labarai ta kasar. Sojoji suka lakada masa duka da kulakai shi da wani abokin aikinsa na Zimbabwe, suka kwace kudaden su,da woyoyi, da kuma katin aikin jarida.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG