Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rishi Sunak Ya Fice Daga Fadar Gwamnati Bayan Da Jam'iyyar Labour Ta Lashe Zabe A Birtaniya


Zaben Birtaniya 2024
Zaben Birtaniya 2024

Jam'iyyar Labour ta Birtaniya ta karbe mulki a yau Juma'a bayan shafe sama da shekaru goma tana adawa, yayin da 'yan adawa suka bai wa jam'iyyar gagarumar nasara.

Sai dai masu lura da a'lamura na cewa akwai babban aiki a gaban su na sake farfado da tattalin arzikin kasar da ya durkushe cikin shekarun da suka gabata.

Keir Starmer ya lashe zaben
Keir Starmer ya lashe zaben

Shugaban jam'iyyar Labour Keir Starmer ne zai zama Firaiminista a hukumance a ranar Juma'a, wanda zai jagoranci jam'iyyarsa ta komawa gwamnati, kasa da shekaru biyar bayan ta sha kaye mafi muni cikin kusan karni guda.

Starmer zai karbi ragamar mulki a fadar 10 gwamnati da ke Downing St. sa'o'i bayan an kirga kuri'un ranar Alhamis.

Starmer da Sarki CHarles III
Starmer da Sarki CHarles III

Rahotanni sun yi nuni da cewa, firaiminista Rishi Sunak har ya kama hanyar zuwa fadar Buckingham don ba da takardar murabus dinsa ga Sarki Charles III.

Rishi Sunak
Rishi Sunak

"Wannan rana ce mai wahala, amma na bar wannan aikin, cikin girmamawa na zama Firaminista a mafi kyawun ƙasa a duniya," in ji Sunak a cikin jawabinsa na ƙarshe a wajen gidan gwamnati.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG