Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS, ta kawo karshen taronta a Abuja, Najeriya.
An yi taron ne a karo na 52 inda aka yi kira ga mambobin kungiyar da su ci gaba da marawa kungiyar baya.
“Akwai bukatar wannan kungiyar ta ci gaba da aiki tare da nuna hadin kai domin cimma muradunta.” Inji Faure Gnassingbe, shugaban kungiyar ta ECOWAS.
Taron har ila yau ya tabo batun rikicin siyasar Togo da na Guinea-Bissau.
‘Yan adawa a kasar ta Togo na neman shugaban kasar Gnassingbe, wanda shi ne shugaban kungiyar ta ECOWAS ya sauka a mulki domin a samar da tsarin yin wa’adi biyu.
Maihaifin Faure, ya kwashe shekau 38 yana mulkar kasar, kafin ya rasu a shekarar 2005, inda dansa ya gaje shi.
Wannan lamari ya sa kasar take fuskantar matsaloli inda a ranar Asabar wasu suka gudanar da zanga zanga a Lome, babban Birnin kasar da zimmar janyo hankalin taron da ya wakana a Abuja.
“Ina kira ga al’umar Togo da su rungumi tattaunawa a matsayin hanyar samar da zaman lafiya.” Inji shugaban Najeriya Muhammad Buhari yayin da yake gabatar da jawabinsa na maraba a gaban taron.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina domin cikakken bayani:
Facebook Forum