Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Fasa-kwauri Ya Yi Sanadin Rufe Sama Da Gidajen Mai 1,800 A Arewa Maso Gabashin Najeriya


Wani Gidan Man Fetur A Najeriya
Wani Gidan Man Fetur A Najeriya

Kusan gidajen mai 2,000 ne aka rufe a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya domin nuna adawa da shirin yaki da fasa kwaurin da hukumomi ke yi wa wasu dillalan man fetur.

Shugaban kungiyar dilalan man fetur, Dahiru Buba ne ya sanar da hakan a ranar Litinin din da ta gabata. Lamarin da ya tilasta wa masu ababen hawa sayen man daga wajen ‘yan bumburutu.

Shugaban kungiyar dillalan man fetur mai zaman kan ta IPMAN na jihohin Adamawa da Taraba Dahiru Buba, ya ce gidajen man sun daina aiki bayan da hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya ta kama tankokin mai ta kuma rufe wasu gidajen mai bisa zargin suna safarar man fetur zuwa makwabciyar kasar Kamaru.

Masu sayar da mai a kasuwar bayan fagge a kasashen Kamaru, Benin da Togo sun kwashe shekaru suna dogaro da man fetur da iskar gas da aka yi fasakwaurinsu daga Najeriya.

A lokacin da gwamnatin Najeriya ta soke tallafin man fetur a shekarar da ta gabata, kasuwanci a kasuwannin na bayan fagge ya durkushe. Amma farashin man ya sake yin arha bayan Najeriya ta kara tsadar tun watan Yunin 2023 duk da cewa darajar kudinta ya ragu sosai.

A karkashin wani shirin yaki da hana fasa kwauri da Hukumar Kwastam ta yi wa lakabin “Operation Whirlwind” ta kama wasu motocin dakon man mallakin kungiyar IPMAN kana suka sake su bayan da ‘yan kungiyar suka rufe gidajen mansu.

A cewar Buba an kuma kwace Karin motocin dakon man, sannan aka rufe wasu gidajen man, lamarin da tilastawa masu gidajen man rurrufe gidajen mansu don nuna rashin amincewa.

“Mun sake rubuta wa Hukumar Kwastam ta Najeriya amma bamu samu martini ba, shi ya sa muka yanke shawarar shiga yajin aikin,” in ji shi, inda ya ce sama da 1,800 na gidajen man sun daina aiki.

"Wannan ita ce sana'ar mu kuma ba za mu yi shiru ba idan ana ci wa mambobinmu zarafi."

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG