Tashin hankali ya karu a cikin 'yan shekarun baya-baya a jihar Benue yayin da karuwar yawan jama'a ke haddasa fadada filayen noma, lamarin da ya sa babu filayen kiwo sosai don makiyaya.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Benue Catherine Anene, ta ce an gano gawarwaki 28 a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Mgban tsakanin yammacin ranar Juma’a zuwa safiyar Asabar.
Nan take dai ba a san dalilin harin ba amma wadanda suka shaida lamarin sun ce ‘yan bindigar sun je wurin ne suka fara harbe-harbe tare da kashe mutane da yawa.
Wannan na zuwa ne bayan wani lamari na dabam da ya faru a jihar a ranar Laraba a kauyen Umogidi da ke karamar hukumar Otukpo, lokacin da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kashe mazauna kauyen a wurin wani taron jana’iza, abinda Bako Eje, shugaban karamar Otukpo, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters kenan.
A wata sanarwa da aka fidda ranar Asabar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen gomman mutane da aka yi a jihar Benue a kwanan nan a yankin Umogidi, ya kuma umurci jami’an tsaro su kara sa ido a yankunan da lamarin ya shafa.