Reverend Danjuma, na majami'ar ECWA Bishara Hausa dake Kano, ya yaba da zaman lafiya da kwanciyar hankalin da aka fara samu a arewacin Najeriya, inda har yanzu Musulmi da Kirista duk sun fara sakewa wajen gudanar da ayyukansu na ibada, da kuma harkokinsu na yau da kullum.
Jami'in, ya ce Musulmi dan'uwan Kirista ne, kuma abokin zamansa, kuma bai kamata a ce ma an samu wani sabani a tsakaninsu ko zamantakewarsu ba.
Yayi addu'ar Allah Ya kawo zaman lafiya a yankin arewacin Najeriya, yana mai rokon Kirista da Musulmi da a koma ga Allah, a ci gaba da addu'ar neman zaman lafiya domin in an yi hakan, lallai za a samu zaman lafiya a kasa.
Reverend Danjuma Adamu ya taya Musulmi murnar shiga wata mai albarka na Ramadan, yana mai cewa, "muna yin addu'a domin su 'yan'uwanmu, abokan zamanmu (Musulmi) su gama wannan ibada da suka dauka ta wata guda a saboda umurnin Allah a kansu, yadda zasu gama shi lafiya."
Yayi rokon da kada 'yan arewa su bar wata kofar da mugunta zata shiga tsakaninsu har ta kawo sabani da rikirkicewa.
Ga dai cikakken bayanin na Reveren Danjuma Adamu, ECWA Bishara Hausa Lamba 1, Kano.