Hajiya Nana Shettima, tana wannan rokon ne a lokacin da take raba agajin abinci, da sutura da kuma kudi ga yara marayu su 100, da kuma mata 100 wadanda suka rasa mazajensu a wajen wani taro a Maiduguri, babban birnin jihar.
Ta ce yana da zafi sosai irin halin da wadannan mata da kuma 'ya'yansu suka shiga ciki a saboda a tsarin rayuwa irin ta yankin, mazajen ne da ma suke dauke da nauyin samarwa da iyalansu abinci da sutura da wurin kwana, amma rashinsu ya sa matan da kuma marayun sun shiga cikin ukuba.
Shi ma shugaban wannan gidauniya ta SWAT, Alhaji Mohammed Bello, yayi kira ga jama'a da su ji tsoron Allah, yana mai fadin cewa irin wannan fitina dake addabar maiduguri da Borno da makwabtanta, sai dai a ci gaba da addu'ar Allah Ya kawo karshen wannan masifa da ta faru.
Gidauniyar ta raba buhu 100 na shinkafa, da buhu 100 na sukari, sannan ta rarraba atamfofi bibbiyu da yadunan shadda goma-goma da kudi Naira dubu uku-uku ga wadannan marayu da matan.
Wadanda suka samu wannan tallafi dai sun bayyana godiyarsu da irin karimcin da uwargidan gwamnan ta yi musu.