Amirar ta ce Allah Ya halicci mutane dabam-dabam, Ya ba su harsuna dabam-dabam, da zabin bin addinai dabam-dabam, da launi da kuma siffa dabam-dabam, domin su zauna da juna su fahimci junansu.
Ta ce Allah ne Ya halicci kowa da komai, yake da iko a kan kowa da komai, don haka ya zamo wajibi mutum ya sao sauran halittun da Allah Yayi.
Ta ce Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) yace imanin mutum ba zai cika ba, har sai ya so ma dan'uwansu abubuwan alkhairi da yake so ma kansa. To wajibi ashe dukkan al'umma na duniya su zauna zaman lafiya da junansu, a samu zaman lafiya a kowane gida da unguwa da gari da kasa a duniya.
Ga cikakken bayanin Amira Rabi'atu Sufyan Ahmad.