Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Lashe Kofin Gasar UEFA Na Bana


Real Madrid lokacin da ta daga kofin 2021/2022 UEFA
Real Madrid lokacin da ta daga kofin 2021/2022 UEFA

Wannan shi ne karo na 14 da Madrid take lashe kofin na Champions League.

Real Madrid ta lashe kofin gasar zakarun nahiyar turai ta UEFA bayan da ta doke Liverpool da ci 1-0.

Dan wasan Real Madrid Vinicius Junior ne ya zura kwallon a ragar Liverpool a minti na 59 bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

An kwashe tsawon zangon farko na wasan, wanda aka buga a filin wasa na Stade de France da ke birnin Paris ba tare da an ci kwallo ko daya ba.

Ko da yake, Karim Benzema ya ci kwallo daya amma alkalin wasa ya soke kwallon saboda satar gida da aka ce ya yi, hukuncin da ya dauki dan tsawon lokaci kafin a yanke shi.

An dan samu jinkirin fara wasan da minti 30 bayan da hukumomi suka ce ‘yan kallo ba su gama shiga filin wasan ba.

Sai dai wasu hotunan bidiyo da suka yi ta yawo a kafar sada zumunta, sun nuna yadda ‘yan kallo musamman na Liverpool suka yi turmutsitsi a wajen filin wasan suna kokarin shiga, lamarin da rahotanni suka ce ya kai ga ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa su.

Wannan shi ne karo na 14 da Madrid take lashe kofin na gasar zakarun nahiyar turai.

Sau shida Liverpool tana lashe kofin.

Har ila yau wannan shi ne karo na uku da bangarorin biyu suke haduwa a a wasan karshe na gasar ta Champions League.

A 1981 Liverpool ta doke Real Madrid a Paris, sannan Real Madrid ta rama a 2018 Kyiv, yanzu kuma ga shi ta lashe wannan karo na uku.

Ita dai Liverpool tuni ta lashe kofin FA Cup da League Cup a can gida Ingila.

XS
SM
MD
LG