Rahotanni daga Najeriya na cewa 'yan bindigar da suka sace daliban kwalejin horar da sha'anin gandun daji dake Afaka a karamar hukumar Igabin jihar Kaduna sun saki dalibai 27.
Sako daliban na zuwa ne, kasa da sa'a 24 bayan da a ranar Talata iyayen daliban suka gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar dokokin kasar da ke Abuja, babban birnin kasar, inda suka nemi gwamnati ta kai masu dauki.
Wakilin Muryar Amurka Isah Lawal Ikara da ke Kaduna ya ruwaito cewa daliban na kan hanyarsu ta komawa garin Kaduna.
Asalin adadin daliban da aka sace a ranar 11 ga watan Maris 39 ne.
Amma a kwanakin bayan an saki 10 daga cikinsu bayan da aka biya kudaden fansa kamar yadda bayanai suka nuna.
Jaridar Daily Trust ta ce, kwamitin sulhu na fitaccen malamin addinin Islama Sheikh Ahmad Gumi ne tare da hadin gwiwar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo suka taimaka aka sako daliban.
Sai dai wasu rahotanni sun ce daliban da aka sako 29 ne kamar yadda Channels ta ruwaito Mr Abudllahi Usman, wanda shi ne shugaban kwamitin iyayen daliban.
Rahotanni sun ce an saki daliban ne a yankin Kidanda da ke karamar hukumar Giwa a jihar ta Kaduna wacce ke arewa maso yammacin Najeriya da ,isalin karfe hudu na yammacin Laraba.
Sai dai babu wasu bayanai da suka nuna cewa an biya kudaden fansa kafin sakin daliban, wadanda maharani suka nemi naira miliyan 500 tun da farko.