A hirar shi da manema labari jim kadan bayan sako daliban, kwamishinan tsaro malam Samuel Aruwan ya ce sai yau Alhamis ne za a mikawa iyayen su bayan duba lafiyar su.
Dr. Ahmad Abubakar Gumi ya tabbatarwa da Muryar Amurka cewa kwamitin da su ka kafa ne ya ceto wadannan dalibai.
Shugaban kungiyar iyayen daliban da aka sace Malam Abdullahi Usman Tumburkai ya ce ba su biya ko sisi ba wajen ganin an sako wadannan yara.
To ko yaya masana harkokin tsaro ke ganin irin wannan lamari, Manjo Yahya Shinko mai ritaya ya ce gaskiyan magana, gwanmati ba abun da ta yi wajen kwato yaran da aka yi garkuwa da su, bai kamata a ce sai na waje ne suka hada kai, aka ceto su ba.
Karin bayani akan: Samuel Aruwan, Malam Abdullahi Usman Tumburkai, Muryar Amurka, Nigeria, da Najeriya.
Wadannan dalibai dai su ne mafi dadewa a hannun 'yan-bindiga cikin daliban da aka sace a 'yan kwanakin nan a jihohin Arewa maso yammacin Najeriya saboda kwanan su hamsin da shidda ba su dawo ba.
Saurari cikakken rahoton a sauti: