Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Aikin Yi Da Matakan Tsaro A Daji Ka Iya Zama Dalilin Cigaban Ayukkan Ta'addanci


Wasu yan bindiga da aka kama
Wasu yan bindiga da aka kama

Wasu da ake tuhumar barayin daji ne, sun bayyana cewa bisa ga tilas ne suke aikata ayukkan ta'addanci saboda koda yaushe a daji suke zaune kuma nan ne suke samun abin dogaro da kai, sannan kuma a nan ne ake shirya munanan ayukka da barayin ke gudanarwa.

Wannan na zuwa ne lokacin da masana lamurran tsaro ke ganin rashin aiki da shawarar samar da rundunar tsaro a cikin daji kan iya zama dalilin da yasa ayukkan ta'addancin yaki ci yaki cinyewa.

An kwashe shekaru 'yan Najeriya na kokawa a kan yadda ayukkan 'yan bindiga ke addabar jama'a musamman a yankin arewa, duk da yake mahukunta na daukar matakan dakile ayukkan na 'yan bindiga.

Daga cikin kokarin da mahukunta ke yi, jami'an tsaro sun yi ta kashewa da kama barayin dajin amma har yanzu ba a samu nasarar dakile ayukkan na su baki daya ba.

Wasu barayin da rundunar 'yan sanda ta kama a Sakkwato sun yi ikirari a kan ayukkan da suke aikatawa da kuma dalilansu.

A hirarsa da Muryar Amurka, daya daga cikinsu mai suna Shehu ya ce bisa tilas ne suke zama da barayin a daji saboda nan ne suke sana'o'insu kuma duk wanda ya bayar da bayani ga mahukunta a kan barayin, nan take zasu kashe shi, saboda haka dole ne zama da su a cikin daji.

Wannan kan iya kasancewa manuniya akan muhimmancin shawarar da masana tsaro kamar Detective Awwal Bala Dirimin Iya ke bayarwa ta a samar da rundunar tsaro ta cikin daji.

To sai dai jami'an tsaron na ganin cewa ayukkan masu tseguntawa barayi bayanai sun fi kawo musu cikas ga ayukan su, a cewar kwamishinan 'yan sanda a jihar Sakkwato, Ali Hayatu Kaigama.

A nasu haujin, mahukunta jinjina suke kara yi ga jami'an tsaro saboda nasarorin da suke samu a kan 'yan ta'adda, tare da alwashin kara bayar da goyon baya ga jami'an, kamar yadda Kanal Ahmad A. Usman mai ritaya, mataimaki na musamman ga gwamnan Sakkwato a kan lamurran tsaro ya nuna a lokacin da ya ziyarci hedikwatar rundunar 'yan sanda da ke Sakkwato.

Da yake shirye shirye sun kankama tsakanin gwamnatocin jihohin Arewa Maso Yamma na daukar matakan kawar da ayukkan 'yan bindiga ta hanyar kafa rundunonin tsaro, watakila gwada amfani da shawarwarin masana kan iya taimakawa ga samun nasara.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG