Rundunar sojan Turai ta NATO tace zata kara kwannaki casa'in ga zamantan a kasar Libya tunda shugaban kasar Muammar Ghadafi yaki sauka daga karagarsa ta mulki. Babban sakataren NATO, Anders Fogh Rasmussen yace sun dauki matakan tsawaita zaman nasu ne don aikawa Ghadafi sakon cewa ba zasu sassabta matsin lambar ganin ya sauka ba. A da, jadawalin da aka shata na hana zirga-zirgar jiragen Libya a cikin sararin samaniyarta a karshen watan nan na Yuni ya kamata ta kare, to amma yanzu wannan karin lokacin yana nufin ke nan za’a ci gaba da yakin har sai cikin watan Satumba
Rundunar sojan Turai ta NATO tace zata kara kwannaki 90 ga zamantan a kasar Libya tunda shugaban kasar Muammar Ghadafi yaki sauka daga karagarsa ta mulki.