Firayim minista Vladimir Putin na Rasha ya tabbatar da cewa lallai zai yi takarar kujerar shugaban kasa a zaben watan Maris, a bayan da shugaba Dmitry Medvedev ya gabatar da shawara a yau asabar cewa ya kamata firayim ministan yayi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2012.
Wannan, kusan ya tabbatar da cewa Mr. Putin dai zai koma kan wannan kujera shekaru hudu bayan da doka ta tilasta masa sauka. Kuri'un neman ra'ayoyin jama'a a Rasha, sun nuna cewa lallai Mr. Putin zai lashe wannan zabe cikin sauki, abinda zai kara karfin tasirin siyasarsa.
Shugaba Medvedev ya fadawa taron shekara shekara na jam’iyyar United Russia mai mulkin kasar cewa a shirye yake ya rungumi wani abinda ya kira aikin zahiri a cikin gwamnati a bayan zaben shugaban kasa na watan maris.
Mr. Putin ya fadawa wakilan taro na jam’iyyar cewa zai gabatar da shawarar Mr. Medvedev ya jagoranci jerin sunayen ‘ya’yan jam’iyyar a zabe ya kuma zamo firayim minista a sabuwar gwamnatin shugaba Putin.
A karkashin sabbin sauye-sauyen tsarin mulkin da Mr. Medvedev ya gabatar, sabon shugaba zai hau kujera na wa’adins hekaru 6 ne maimakon shekaru 4 da ake yi yanzu.