Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Sake Hawa Kujerar Naki Kan Syria


Russia US
Russia US

A jiya laraba ne kasar Rasha ta sake hawa kujerar naki domin kare shugaban kasar Syria Bashar Al-Assad, daga sukar da yake sha daga kasashen duniya game da harin makami mai guba.

Da wannan matakin na kasar Rasha, hakan yana nufin Kenan ba zata bada bayanai, ko hadin kai ba, ga duk wani kwamitin bincike mai zaman kansa da MMD zata kafa, har ma da wani matakin da zata dauka wanda ka iya taimakawa domin samun zaman lafiya ga kasar ta Syria.

Wadannan kalaman dai suna fitowa ne daga bakin jakadiyar Amurka a MDD, Nikki Heyli sailin da take Magana a azure taron MDD. Tace har wayau Rasha ta zabi marawa Assad baya.

A kuri’un 10 da ake dasu, biyu sun jefa kin amincewa, kana ukku suka kaurace, yayin da Moscow ta toshe damar da Birtaniya, Faransa da Amurka suke da shi, China dama abu ne mawuyaci ta ba Rasha baya, ita taki jefa kuria’ar, yayin da sauran wadanda basu da kujeran din-din-din irin su Bolivia, sun jefa kin amincewa ne yayin da Ethiopia da Kazakhastan suka bi sahun China na kin jefa kuriaar.

Shi dai wannan kudiri manufar sa ita ce shine yin ALLAH Waddarai da harin makami mai guba kana a samar da kwamitin bincike mai karfin gaske domin gane abinda ya faru game da wannan harin.

wannan kuriaar da aka jefa dai ba shine na farko ba domin ko a ranar alhamis din data shige sai da aka yi irin wannan yunkurin amma hakan bai cimma nasara ba.

Heyli tace idan dai gwamnatin ta Syria da gaske take yi bata da masaniya kamar yadda Rasha ta kasa ta tsare, to bayanan da za samu samakon binciken shine zai fidda Gaskiya al’amari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG