Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Sa Sunan Mai Dakin Marigayi Alexey Navalny Cikin Jerin Sunayen Wadanda Ta Ke Zargi Da Ta’addanci:


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

A ranar Alhamis ne Rasha sa sanya sunan Yulia Navalnaya, wata fitacciyar yar adawa a Rasha, kuma mai dakin marigayi Alexey Navalny, kan jadawalin ta na jerin sunayen 'yan taadda da masu tsatstsauran ra’ayi.

Sanya sunan Navalnaya a jadawalin masu bakin fentin na nufin, akwai yiwuwar aza takunkumi kan huldar da zata yi da bankuna, wani abu da sauran 'yan adawa da aka yima irin wannan shaida suka fuskanta.

Bakanta sunan yazo ne kwanaki biyu bayan da jami’an Rashan sun bada umurnin kama Navalnaya, bisa zarge zargen shigar ta wata kungiyar masu tsatstsauran ra’ayi. Navalnaya na zaman gudun hijira ne a Jamus, kuma za a kama ta da zaran ta dawo Rasha.

Har yanzu dai jami’ai basu fito fili a hukumance sun fadi takamamiyar hujja bisa zarge zargen da ake ma Navalnaya ba.

Navalnaya, mai shekaru 47 a duniya tayi alkawarin dorawa kan aikin da mai gidanta, babban mai caccakar shugaban Rasha Vladimir Putin, wanda ya rasu a wani gidan kaso a Siberiya yayin da yake zaman daurin shekaru 19 bisa zarge zargen tsatstsauran ra’ayi. Jami’an Rasha sun bayyana cewa, Navalny ya kamu da rashin lafiya, bayan wani tattaki da yayi cikin yanayi na tsananin sanyi da ya yi sanadiyyar mutuwar shi. Mai dakin shi Navalnaya, ta bayyana imanin cewa, an dai azabtar da maigidan nata ne da kuma barin shi da yunwa.

Shugaban Jamus Olaf Scholz ya caccaki yunkurin na Rasha na bada umurnin kama Navalnaya, a matsayin abinda ya sabawa democradiyya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG