Jami'an Ukraine sun ce Rasha ta kai hari kan babban birnin kasar Kyiv da wasu garuruwa hudu da suka hada da - Dnipro, Kryvyi Rih, Slovyansk da kuma Kramatorsk.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce Rasha ta kai hare-hare da rana da makamai masu linzami sama da 40 a biranen biyar, harin da ya afka kan wasu gidaje da kayayyakin more rayuwa. Sojojin saman Ukraine sun ce sun kakkabo makamai masu linzami guda 30.
Kakakin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya ce, Sakatare-Janar din Antonio Guterres ya yi Allah wadai da hare-haren, yana mai cewa hare-haren da aka kai a cibiyoyin kiwon lafiya "abin damuwa ne matuka"
Ita ma Amurka ta yi Allah-wadai da harin da Rasha ta kai a asibitin yara da ke birnin Kyiv da sauran wurare.
Dandalin Mu Tattauna