Cikin wadanda wannan mataki zai shafa harda tsohon darektan hukumar leken asirin Amurka CIA John Brennan, da kuma tsohon darektan hukumar binciken manyan laifuffuka FBI James Comey.
Galibin wadannan mutane da suke da izinin samun bayanan sirri na gwamnati suna fitowa a talabijin suna sukar gwamnatin ta yanzu.
Trump ya kai ha wuya kan kalaman tsohon darektan na CIA Brennan, wand a a shafin Twitter ya caccaki taro da manem alabarai d a Mr. Trump yayi tareda shugaban Rasha Vladimir Putin a Helsinki. Brennan yace "maratnin da Trump ya bayar na watakil goyon bayan Putin, ba karamin laifi bane, ya kai mizanin ace cin amanar kasa. Ya kara da cewa ba kurum kalaman Trump suna cike da yarantaka Putin ya mallaki Trump."
Tsohon darektan hukumar leken asiri ta na'ura, James Clapper, shima yana cikin jerin tsoffin jami'an gwamnati da Trump yake shirin karbe ikonsa na sanin sirrin gwamnati. Clapper ya gayawa CNN cewa karbe ikon ba wani abu ne hali karamin mutum a zaman gayya saboda sukar lamirin gwamnati.
Facebook Forum