Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Da Najeriya Za Su Samar Da Tashoshin Wutar Lantarki Na Makamashin Nukiliya


Gwamnatin Najeriya da wani kanfanin kasar rasha sun rattaba hannu wajan gina tashoshin samar da wutar lantarki mai anfani da makamashin nukiliya a kasar.

Wannan inji hukumar kula da makamashin Nukiliya ta Najeriya zai taimaka wajen samar da mega-watt fiye da 4500, na wutar lantarki a fadin kasa a wata yarjejeniya da aka fara tun a shekara ta 2015, ta samar da tashoshin Nukiliya gud hudu da aka ce kudin su zai kai dalar Amurka Biliyan Ashirin.

‘Yan Najeriya da sauran masana sun yi ittifakin cewa matsalar rashin cigaban Najeriya na da nasaba da karancin wutar lantarki wanda kawo yanzu gwamnatin kasar ta ce tana kan kokarin samar da Mega-watt 4500, karfin wutar lantarkin da masana ke ganin ya yiwa kasar kadan idan aka yi la’akari da girman al’ummar da kuma wutar da wasu kasashe da basu kai girman Najeriyar ba ke samarwa.

Mr Baba Tunde Raji Fashola, shine ministan wutar lantarki da ayyuka da gidaje, ya bayyana cewa akwai matsaloli da dama da ake fuskanta kuma gwamnati na iyakacin bakin kokarinta wajan ganin ta magance matsalolin a gajeren lokaci mai zuwa.

Sai dai kuma a yayin da gwamnatin ke kokarin samar da wannan makamashi wajan samar da wutar lantarki, masana harkokin wutar lantarki sun bayyana cewa kamata yayi gwamnati ta ayi amfani da sauran makamashi da take da shi a kasar kamar yadda farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji na jami’ar kimiyya da fasaha na jihar Neja ya bayyana.

wakilinmu na Legas Babangida Jibrin ya ji ta bakin masana game da wannan shiri.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG