Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Shida Sun Mutu, A Harin Mota Da Kuma Harbe-Harbe A New York


Rahotanni daga kafofin yada labarai da dama na Amurka sun ce mutane da yawa sun ji rauni cikin daren nan agogon Najeriya a gundumar Manhattan ta birnin New York, a bayan da 'yan sanda suka tabbatar da cewa su na binciken rahotannin harbe-harbe.

Hukumar 'yan sanda ta birnin New York, NYPD, ta buga a shafinta na Twitter cewa an kama mutum daya ana tsare da shi.

Hukumar NYPD ta ce wata motar a-kori-kura ta bi ta kan hanyar da aka ware ma masu kekuna a kusa da Cibiyar Cinikayya ta Duniya, ta taka mutane da yawa. Rahotanni suka ce mutane shida suka mutu, sha daya suka ji rauni.

Jaridar New York Times ta ce motar a-kori-kurar ta kuma kara da wata bas ta 'yan makaranta.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG