Jami’an hukumar kwastan ta Najeriya a shiyyar Jihohin Kano da Jigawa sunce sun kama akwatuna ashirin na magunguna da kayan abinci da ake fasa kwaurinsu ta kan iyakar Najeriya da Nijar ta bangaren jihar Jigawa
A yayin taro da manema labarai a Kano, shugaban hukumar kwastam mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Yusuf Abba Kasim, ya ce wasu mazauna karkara ne suka tseguntawa Jami’an hukumar game da yadda masu fasa-kwaurin wani magani da ake kira Tramol da a halin yanzu wasu suka maida shi kayan maye, suka tara da zummar shigar dasu kasuwa.
Haka zalika, Yusuf Abba Kasim ya ce Jami’an sun kama wani adadin na buhunan shinkafa da masu fasa-kwaurin suka shigo da ita cikin Najeriya, duk da cewa, gwamnatin tarayya ta haramta safarar ta ta kan iyakoki fiye da shekaru biyu da suka gabata.
Da yake amsa tambaya akan abinda Hukumar Kwastan take da kayan da take kamawa, Yusuf Abba Kasim ya ce sukan tura magunguna zuwa ga NDLEA, hukumar dake hana safarar miyagun kwayoyi. Idan kuma abinci ne sai su ba gwamnati wadda sau tari ta kan rabawa sansanin ‘yan gudun hijira.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani
Facebook Forum