Shan magungunan tari kamar su benelin, da kodin da wiwi da koken da ma wasu dabaru da matasa ke yi su kan birkitar da hankulan mutane su maida su wani abu daban. Kamar yadda masanin magunguna Haruna Aliyu na ma'aikatar kiwon lafiya a Jihar Neja ya fada masu shan magungunan tari ba tare da kamuwa da tarin ba su kan samu tabuwar hankali. Wani lokacin ma abun na shafar nufanshisu har ma ya kaiga mutuwa idan ba'a ci sa'a ba.
Da alamu wannan ranar ta dauki hankalin duk wani wanda yake gani yana da takarawar da zai iya yi game da dakile anfani da miyagun kwayoyi. Sani Abdullahi Zakari kwamandan mayakan sama dake garin Minna ya ce suna hada hannu da Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) shi ne ma yasa suka amsa gayyatar da aka yi masu zuwa taron gangamin. Ya ce suna hana shan kwaya a barikokinsu suna sa ido kan wuraren dake kusa da su. Shi ma Danladi Abdullahi sakataren kungiyar direbobi masu daukar fasinjoji ya ce basa bari duk wani direba dake shan kwaya mai sa maye ya tuka mota balantana ma a bari ya dauki fasinjoji.
Wani Hassan Mohammed matashi da aka same shi a gidan yara cewa ya yi a daure aka kawo sh gidan lokacin da yake cikin maye. Ya ce bai san lokacin da ya zo gidan ba domin yana shan wiwi da kodin da sigari abubuwan da ya ce abokanan banza suka sa shi yi.
Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta ce tana samun nasara a yakin da take yi domin ko a Jihar Neja ta kama mutane fiye da sittin a jihar. Ita hukumar ta shiga jerin gwano a titunan Minna tare da zuwa makarantu gaba da firamare domin fadakar da kawunan matasa.
Wakilinmu Mustafa Nasiru Batsari na da karin bayani.