A jihar Neja gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa dake taya Ibrahim Idris murna bisa ga sabon mukamin da ya samu.
Duk da tayashi murma kwamishanan yada labarai na jihar Neja Mr. Jonathan Batsa yace akwai kalubale a gaban sabon babban sifeton a daidai wannan lokacin. Yace, misali a arewacin kasar, musamman a jihar Neja wadda sabon babban sifeton dan asalinta ne, akwai sace mutane da satar shanu da fashi da makami da yawan kashe-kashe da yanzu suke tadawa jama'a hankali.
Manoma da makiyaya suna yawan fada da juna ba ma a jihar Neja kadai ba har da wasu jihohin kasar. Kwamishana Batsa yace suna fata Allah ya sa sabon babban sifeton ya maida hankali akan irin wadannan matsalolin. Yana fatan zai taka rawar gani har jama'a zasu ce a lokacinsa 'yansanda sun canza hali.
'Yan agaji dake taimakawa jama'a tare da sanya idanu domin tabbatar da tsaro a lokacin taron jama'a sun yi maraba da sabon shugaban 'yansandan.
To saidai shugaban bada agaji na kungiyar IZALA, Injiniya Mustapha Imam Sutti yace suna da roko ga sabon shugaban na 'yansandan.Ya kirashi ya maida hankalinsa akan abun da ya shafi tsaro. Ya kuma maida hankalinsa akan cin hanci da rashawa da ya yiwa 'yansandan katutu. 'Yansanda da suke tsayawa akan tituna miyagun mutane dauke da makamai akan barsu su wuce da zara sun bada cin hancin nera ishirin ko hamsin.
Dangane da daukan sabbin 'yansanda aiki masana harkokin tsaro sun kira shugaban na 'yansanda da ya gudanar da binciken kwakwaf akan duk wanda ya nemi shiga aikin 'yansanda domin gudun daukan kara da kiyashi cikin jama'a.
Ga karin bayani.