Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Afirka Uku Ba Zasu Goyi Bayan Amurka Ba Domin Ta Basu Taimako


Nikki Haley jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya
Nikki Haley jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya

Ta'allaka bada taimako ga kasashe masu tasowa da irin goyon bayan da suke baiwa Amurka da jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley tayi, ya sa wasu kasashe uku suka sake jaddada matsayinsu na kin goyon bayan Amurkan saboda taimakon da zata basu

Wasu kasashe uku a Afrika da basu goyon bayan Amurka a duk kuri’ar da ake kadawa a Majlaidsar Dinkin Duniya, sun ce suna kan bakansu, koda kuwa rashin goyawa Amurka baya zai yi dalilin yanke taimako da take musu.


Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, MDD Nikki Haley tayi barazanan yanke taimako da Amurka ke baiwa kasashen ne a cikin wata sanarwa a makon da ya gabata biyo bayan rahoton shekara da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a kan yanda kasashe ke kada kuria a MDD


Jerin sunayen kasashe da ma’aikatar harkokin wajen ta fitar na bana ya hada da Burundi da Afrika ta Kudu da kuma Zimbabwe.

Ga dai martani da martanin mai Magana da yawun gwamnatin Zimbabwe George Charamba a kan kalaman Haley.


Shiko mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Afrika ta Kudu Ndivhuwo Mabaya yace Afrika ta Kudu ba zata karaya ba.

Yace bai yiwuwa a ta’allaka harkokin diplomasiya akan bada cin hanci ba, idan baku goyi bayanmu ba, ba zamu baku kudi ba. Wannan wani matsayin diplomaisya ne da Afrika ta Kudu ba zata saka kanta a ciki ba. A matsayinmu na kasa mai cin gashin kai, muna da ra’ayinmu a kan kowane batu da zai taso. Yace muna da bukatun ta kasa kuma akwai bukatarmu a kungiyar raya kasashen mu da ake cewa SADC a takaice.

Shi kuwa mai magana da yawun kasar Zimbabwe, Caharamba, bayan y gama dariya, ya bayana dalilin da yasa galibi ra’ayin Zimbabwe ke bambamta da na Amurka.

Yace saboda mu Zimbabwe ne. Ba zamu taba amfani da manufar harkokin wajen wata kasa mai girma ko tasiri, koda kuwa Amurka ce ko kuma wata babar kasa ta dabam. Muna kada kuri’armu ce a bisa ka’ida.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG