Manufar kebe ranar itace tattaunawa tare da bitar matakan kare ma’aikata daga tsangwama da kuma tabbatar da koshin lafiyarsu a lokacin da suke bakin aiki.
Wani rahoto da kungiyar Kwadago ta duniya ta fitar ya nuna cewa kimanin ma’aikata maza da mata Miliyan 2 ne ke rasa rayukansu a kowacce shekara sanadiyar hadura masu nasaba da aiyukansu ko cutuka da suka dauka a bakin aiki.
Rahotan yace ana samun afkuwar hadura a guraren aiki a duniya baki daya har sau Miliyan 270, yayin da ma’aikata Miliyan 160 ke daukar cutuka daban daban a kowacce shekara.
Domin karin bayani.